Ma'aikatar harkokin cikin gida na gwamnatin kasar Sudan ta sanar cewar, a kalla mutane 22 ne suka halaka, ciki har da wani Basarake daga kabilar Dinka Ngok da kuma ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na MDD lokacin wani taho mu gama da ya abku a wurin da ake takaddama dake kan iyaka tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu a jiya Lahadi.
Wannan tashin hankali da ya faru a yankin Abyei, in ji sanarwar, ya yi sanadiyar rasa ran Basaraken kabilar Dinka Ngok, Kual Deng Majok da biyu daga masu rufa masa baya, sannan da mutane 17 daga cikin kabilar Miseriya, sannan an raunata mutane 12, baya ga wassu manyan jami'ai na wanzar da zaman lafiyar MDD na tsaro a yankin.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan ta nuna matukar jimaminta game da wannan al'amari, tana mai kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su yi hakuri da juna, su bar zaman lafiya ya wanzu, ta yadda kwanciyar hankali zai dawo a tsakanin kabilun biyu, musamman ganin yadda tarihi ya nuna zumuncin dake tsakaninsu tun farko.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan ta yi bayanin cewa, wata tawagar basaraken karkashin jagorancin mataimakin shugaban kwamitin hadin gwiwwa, da ya kunshi Sarkin kabilar Ngok, Kual Deng Majok wadanda suka samu kariya daga kwamandan rundunar tsaro na MDD a yankin Manjo Janar Yohannes, 'dan asalin kasar Habasha sun ziyarci garuruwan Guli, Tajalli da kuma Difra da mafi yawansu 'yan kabilar Miseriya ne, ba tare da sun sanar da masu lura da wurin ba.
A cewar ma'aikatar harkokin cikin gidan, wassu gungun matasa daga kabilar Miseriya bisa babura suka tare tawagar da ta kunshi Sarki Kual Deng Majok cewar, sai dai su mayar masu da shanunsu da kabilar Dinka Ngok suka karbe, takaddamar da aka dauki fiye da sa'o'i uku ana yi wanda ya yi sanadiyar musayar wuta tsakaninsu da kuma asarar rayuka a wurin.
Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta yi Allah wadai da wannan abu da ya faru a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi.(Fatimah)