A kwanan baya, an kai hare-hare a jere a jihar Xinjiang ta kasar Sin, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane da yawa, da kuma kawo barazana ga bunkasa tattalin arzikin jihar da hadin kan kabilun jihar. Gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai ga hare-haren, kuma shugabannin kasar Sin sun ba da umurni ga hukumomin da abin ya shafa da su yi nazari kan hare-haren da kuma ayyukan yaki da ta'addanci.
A gun taro kan yaki da ta'addanci da aka shirya a ran 4 ga wata, Meng Jianzhu ya bukaci hukumomi daban daban da abin ya shafa da su aiwatar da matakan yaki da ta'addanci, da yin kokari wajen kiyaye zaman lafiya a jihar.(Abubakar)