Ran 28 ga wata, mataimakin zaunanen wakilin kasar Sin dake MDD Wang Min ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su kawar da ka'idoji mabanbanta kan kasashen duniya a fannin aikin yaki da ta'addanci domin taimakawa kasashe masu tasowa wajen yaki da ta'addanci da karfafa matsayin shugabancin da MDD ke dauka wajen aikin kawar da ta'addanci.
A wannan rana, MDD ta kira taro domin tunawa da ranar cika shekaru 10 da zartas da kuduri na 1373 da kafa kwamitin yaki da ta'addanci. Mr. Wang Min ya furta cewa, kasar Sin ta nuna adawa da bin ma'aunai iri 2 a fannin aikin yaki da ta'addanci, wannan muhimmin dalili ne da ya hana tabbatar da kuduri na 1373. Bai kamata wata kasa ta tsai da ma'aunin tabbatar da wata kungiya a matsayin kungiyar ta'addanci bisa barazanar da ta kawo mata ba. Dole ne kowane mutum da ya aikata laifin ta'addanci bisa kowane dalili zai gamu da hukunci daga gamayyar kasa da kasa.(Lami)