Ranar Laraba 28 ga wata a birnin New York hedkwatar MDD, babban sakataren majalisar malam Ban Ki-Moon ya ce, ta'addanci tamkar wani babban kalubale ne ga duniya, hakan ya sa ya yi kira ga kasashen duniya da su yi kokarin kawar da ta'addanci.
A wannan rana da yamma a gun wani taro na musamman da MDD ta yi, an taya murnar cika shekaru 10 da zartas kuduri mai lamba 1373 tare da kafa kwamitin yaki da ta'addanci. Ban Ki-Moon ya yi jawabi cewa, wannan kuduri ya kasance wani muhimmin aiki ne wajen dakile ta'addanci.
Ban Ki-Moon ya ce, kamar halin da ake ciki a shekaru 10 da suka gabata, ta'addanci ya kawo babbar illa ga duniya, duban mutane sun rasu sakamaon haka. Hare-haren da aka dinga kaiwa, ba ma kawai an yi asarar tattalin arziki ba, har ma sun kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.
Ya ce, babban aiki da aka sa gaba shi ne, kwamitocin dake karkashin kwamitin sulhu su yi hadin kai. Kuma ya yi kira ga kwamitin sulhu da zai taka rawar a zo a gani cikin wannan aiki.(Amina)