Mista Zhang Chunxian ya yi wadannan kalamai a lokacin wani taron da gwamnatin yankin ta kira bayan wasu jerin hare hare ukku da aka kaiwa jihar ta Xinjiang.
Baya da haka mista Zhang ya mika kiransa ga kwararru da ma'aikata da su ba da taimako sosai domin yaki ba tare da kasala ba kan wasu ayyukan addini dake adawa da dokar kasa da kuma ake amfani da addini domin rura wutar gaba tsakanin kabilun kasar da kuma hada kai wajen kai hare haren ta'addanci, in ji kafofin watsa labarai na jihar a ranar yau Litinin. ( Maman Ada)