Bisa wannan daftari, aikin ta'addanci na nufin aikin da zai haddasa hasarar rayukan mutane da ta dukiyoyi da dama da dai sauran ayyukan da za su lalata tsarin zaman al'umma, ta hanyar nuna karfi, lalata kayayyaki da sauransu, da zummar tada zaune tsaye ko yin barazana ga hukumomin kasa ko kungiyoyin duniya. Bugu da kari, aikin tada zaune-tsaye, ba da kudin agaji ga ayyukan da aka ambata a baya da sauransu, su ma ayyukan ta'addanci ne. Kungiyar ta'addanci na nufin kungiyar da aka kafa domin gudanar da aikin ta'addanci, yayin da 'yan ta'adda ke nufin mutane ko membobin kungiyar ta'addanci, wadanda suka tsara, yin fasali, da kuma gudanar da aikin ta'addanci.
Ban da haka, daftarin ya tanadi cewa, yayin da hukumomin 'yan sanda na majalisar gudanarwa ta Sin suka gabatar da sunayen kungiyoyin ta'addanci da na 'yan ta'adda, dole ne su yanke shawarar daskarar da kaddarorin kungiyoyin da na 'yan ta'adda da dai makamantansu.(Fatima)