A wannan rana, an shirya taron M.D.D a karo na 66, inda aka tantance dabarun yaki da ta'addanci. Yayin da Wang Min ya yi jawabi, ya ce, mambobin kasashen M.D.D sun cimma daidaito tsakaninsu kan dabarun yaki da ta'addanci, kuma abin na da muhimmanci sosai. Ya ce, kasar Sin tana fatan kasashen duniya za su kara mai da hankali kan batun kawar da sanadiyar haifar da ta'addanci, da aiwatar da dabarun yaki da ta'addanci cikin daidaito daga dukkan fannoni.
Wang Min ya ce, kasar Sin za ta nace ga yaki da ta'addanci, don tabbatar da tsaron kasa da dukiyar jama'a, da kiyaye hakkin dan Adam, haka kuma, kasar Sin za ta ci gaba da daukar hakikanin matakai don aiwatar da dabarun yaki da ta'addanci na duniya, da inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya wajen yaki da ta'addanci a karkashin inuwar M.D.D. (Bako)