in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Philippines ta ce "watakila" 'yan sanda ne suka harbe wasu daga cikin masu yawon shakatawa daga Hong Kong
2010-09-09 20:47:03 cri

Ran 9 ga wata, kwamitin bincike "kan mutuwar mutane masu 'yan yawon shakatawa da aka yi garkuwa da su a ran 23 ga watan Agusta" a kasar Philipines ya yarda da cewa, watakila 'yan sandan kasar ne suka harbe wasu daga cikin masu yawon shakatawa na yankin Hong Kong na kasar Sin.

Mr. Leila de Lima ministan harkokin shari'a na kasar Philipines wanda ke jagorancin aikin nazarin wannan batu ya bayyana cewa, watakila 'yan sanda ne suka harbe wasu masu yawon shakatawar daga Hong Kong yayin da suke kokarin ceto su. Ban da haka kuma, wasu kwararrun da suke cikin aikin binciken sun tabbatar da cewa, akwai wasu harsasa da ba mai laifin ne ya harba su ba. Game da haka, za a bukaci bangaren 'yan sanda na Hong Kong da ya yi bincike kan batun tare.

A wannan rana, ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Philipines ya bayar da sanarwa cewa, a ran 8 ga wata, shugaba Benigno Aquino lll na kasar Philipines ya gana da jakadan kasar Sin Liu Jianchao inda ya ce, kasar Philipines za ta yi hadin kai da kasar Sin domin daidaita wannan lamari, ta yadda za a samu ci gaban huldar da ke tsakanin kasashen biyu.

Mr. Liu Jianchao ya nuna cewa, yayin da ake yin aikin ceto da ayyukan daidaita lamarin, shugaba Aquino ya ba da umurnin yin bincike daga dukkan fannoni cikin adalci kan lamarin. yanzu kasashen Sin da Philipines suna yin hadin gwiwa wajen gudanar da bincike kan wannan lamari. [Musa Guo]

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China