in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangaren 'yan sanda na Hongkong ya gama aikin neman shaidu game da lamarin yin garkuwa da mutane da ya faru a Philippines
2010-09-18 18:40:05 cri
A ranar 17 ga wata, Gwamnan hukumar yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, Donald Tsang ya bayyana cewa, yanzu bangaren 'yan sanda na Hongkong yana kokarin tattara dukkan shaidu game da lamarin yin garkuwa da wasu mutanen Hongkong da ya faru a kasar Philippines, amma har zuwa yanzu ba a samu rahoton da kwamitin binciken lamarin na kasar Philippines ya gabatar ba.

Donald Tsang ya ce, kafofin watsa lamaru sun bayar da labari cewa, kwamitin yin bincike kan lamarin na kasar Philippines ya riga ya gabatar da wani rahoto ga shugaban kasar, amma shi da kansa bai samu wannan rahoto ba. Ya kara bayyana cewa, bayan da gwamnatin Hongkong ta dudduba wannan sakamakon bincike kuma za ta dauki matakai nan gaba. (BIlkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China