A ranar 17 ga wata, Gwamnan hukumar yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, Donald Tsang ya bayyana cewa, yanzu bangaren 'yan sanda na Hongkong yana kokarin tattara dukkan shaidu game da lamarin garkuwa da wasu mutanen Hongkong da ya faru a kasar Philippines, amma har zuwa yanzu ba a samu rahoton da kwamitin binciken lamarin na kasar Philippines ya gabatar ba.
Dadin dadawa a yau ranar 18 ga wata, mashawarcin shugaban kasar Philippines a fannin sadarwa da tsare tsaren cikin gida, Ricky Carandang ya bayyana cewa, kasar Philippines za ta gabatar da kwafin rahoton bincike ga hukumar kasar Sin a ranar 18 ko 20 ga wata, kuma za ta sanar da abubuwan dake cikin wannan rahoton bincike ga jama'ar kasar Philippines a farkon mako mai zuwa. (BIlkisu)