in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba za a yayatawa duniya batun 'yancin Taiwan ba, in ji Ma Ying-jeou
2013-04-29 16:35:31 cri

Jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Ma Ying-jeou, ya fada a yau Litinin 29 ga wata cewa, yankin na Taiwan ba zai yayata manufar nan ta " Sin daya, Taiwan daya", ko kuma batun "'yancin yankin Taiwan" ba a ciki da wajen yankin.

Ma ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wani biki da asusun musaya tsakanin bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan da ke zaune a Taiwan din ta shirya don murnar cika shekaru 20 da yin shawarwari mai suna "taron Wang-Koo", wanda ya shimfida tubalin ci gaban zaman lafiya.

Ma ya ce, "dukkanmu Sinawa ne kuma muna da tarihi da al'adu guda". Yana mai cewa, babban yankin kasar Sin da na Taiwan sun kafa tarihin sasanta rashin jituwa cikin lumana.

Ma ya ce, yana fatan bangarorin biyu za su ci gaba da zurfafa hadin kai da musaya a fannoni daban-daban, ciki har da tattalin arziki, cinikayya, al'adu, kimiyya da fasaha da kuma muhallin halittu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China