in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 2 na karshe na kungiyar yawon shakatawa da aka yi garkuwa da su a kasar Philippines sun komo yankin Hongkong
2010-08-27 15:38:08 cri

A ran 26 ga wata, saurayin da ya ji rauni a sakamakon batun aka yi garkuwa da motar masu yawon shakatawa na Hongkong da aka yi a kasar Philippines Liang Songxue tare da mahaifiyarsa sun iso yankin Hongkong. Yanzu kenan, dukkan mutanen dake cikin kungiyar 'yan yawon shakatawa da aka yi garkuwa da su tare da gawawwakin sun iso yankin Hongkong.

Babban darektan hukumar kiwon lafiya ta yankin Hongkong Liang Boxian ya bayyana cewa, a cikin jirgin sama na musamman da ya dauko Liang Songxue, akwai na'urar ba da agaji, kuma rukunin likotoci da yankin Hongkong ya aika zai duba lafiyar Liang Songxue. Bayan ya iso yankin Hongkong, an tura Liang Songxue zuwa asibiti na Tunmen don yi masa jiya.

A sa'i daya kuma, bangaren 'yan sanda zai yi binciken kan batun.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China