Wu Sike ya ci gaba da cewa, batun kasar Siriya ya zamo abin da bangarori daban daban ke dora muhimmanci sosai a kai, kuma kasar Sin kullum take tsaye kan ra'ayin warware batun ta hanyar yin shawarwari, ba wai a warware wannan batu ta hanyar karfin soji ko yin shisshigi wa kasar ba.
A sa'i daya kuma, ya ce, a halin da ake ciki yanzu, da wuya ne, a warware batun kasar Siriya ta hanyar siyasa, amma wannan ba wai yana nufin cewa za a yi watsi da wannan hanya ba ne.
kasar Sin za ta dage wajen nuna goyon baya ga rawar da M.D.D. da kungiyar AL suke takawa wajen warware batun Siriya. Haka kuma, Mr. Wu ya jaddada cewa, kasar Sin ba za ta nuna goyon baya ko kuma yin adawa da ko wane bangare ba, kuma za ta yi la'akari ne da moriyar jama'ar kasar Siriya, don sa kaimi ga warware batun ta hanyar siyasa.(Bako)