in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana cigaba da kame dangane da bam din aka dasa a wata mujami'a a Tanzaniya
2013-05-10 10:32:07 cri

A garin Arusha na kasar Tanzaniya, 'yan sanda sun samu nasarar kara kame wassu mutane 3 da ake zargin suna da hannu a harin bam din da aka kai a wata mujami'ar Katolika a ranar Lahadin da ta gabata.

Jami'in 'yan sanda na yankin Arusha kwamanda Liberatus Sabas ya shaida ma manema labarai cewa, a cikin sa'o'i 24, sun sami nasara kame wadanda ake zargi har su 12, kuma a yanzu haka, suna kan gudanar da bincike kafin a gurfanar da su a gaban kuliya.

Sai dai a cewar kwamanda Sabas, bincike ya nuna cewa, wadannan bam din da suka fashe ba kirar hannu ba ne, sannan kuma mutane hudun 'yan asalin kasar Saudiya da aka kama a kan iyakar Namanga dangane da wannan harin, an tabbatar da cewar, suna da cikakkun takardun izinin zama a kasar.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai aka kai harin bam a mujami'ar Katolika dake Arusha wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 3, sannan wadansu fiye da 60 suka samu rauni.

Speto janar 'yan sandan kasar Saidi Mwema ya sanar da kyautar kudin Tanzaniya shillings miliyan 50, kwatankwacin dalar Amurka 31250 ga duk wanda ya taimaka da cikakken bayani game da ayyukan wannan kungiya ta 'yan ta'adda a kasar dake gabashin Afrika.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China