Jami'ai masu kula da ceto sun ce fiye da gawawwaki 190 ne aka tsamo kuma gidan radiyon kasar ta ba da labarin cewar a zuwa wannan lokacin fiye da mutane 620 ne aka ceto su kuma wassu an duba su an sallame su a asibiti wassu kuma an ba su gado a babban asibitin Zanzibar.
Shi dai wannan jirgin da hadarin ya abku da shi an yi shi ne musamman don daukan fasinjoji 610,amma wadanda suka gane ma idon su sun ce akwai yuwuwan fasinjojin sun zarce haka a cikin jirgin lokacin da ya doshi Pemba,wani tsibirin na Zanzibar.
Gidan talabijin din Zanzibar nata nuna fuskokin gawawwakin mutanen kai tsaye saboda dangin su ko za su gane su domin daukan su binne.
Har yanzu akwai dubban mutane da suka yi cicirindo a wani filin dake Stone Town,babban birnin kasar Zanzibar don neman dangin su dake cikin jirgin daya fadi,don an shirya tantin wucin gadi inda aka ajiye gawawwakin wadanda hadarin ya rutsa da su.
Rahotanni dake fitowa ya ce musabbabin hadarin shi ne yawan fasinjoji da kaya da suka wuce kima,Amma wassu rahotannin na cewa tangardar naura ma na iya zama wani dalili. (Fatimah)
Gwamnatin Zanzibar ta bayyana wannan hadarin a matsayin mafi muni kuma bala'in da ya shafi kasar duka