Kafofin yada labaru na wurin suna ganin cewa, sakamakon kokarin kammala ginawa gine-gine cikin sauri wato kafin lokacin da aka tsai da shi ne ya sa ba a sa ido yadda ya kamata kan wasu gine-gine a lokacin da ake gina su, ta haka gine-ginen ba su da inganci sosai, inda lamarin da ya haifar da irin wannan hadari. Kafin wannan lamari na yanzu, an samu hadarurrukan faduwar gine-gine a Dar es Salaam. (Tasallah)