in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzaniya na sha'awar bunkasa dangantaka da Sin, in ji jakadan kasar
2013-03-22 09:52:09 cri

Jakadan kasar Tanzaniya a kasar Habasha, Joram Kiswaro ya ce, kasar tasa na matukar sha'awar bunkasa dangantaka da kasar Sin bisa tubali da wadanda suka kafa kasashen suka gina a shekarun 1960.

Yayin hira da kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua ranar Alhamis, jakadan ya ce, dangantaka tsakanin kasar Sin da Tanzaniya na ci gaba da bunkasuwa duk da sauye-sauye da aka fuskanta.

Ya ce, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta faro ne tun shekarun 1960, bisa kokarin wadanda suka kafa wadannan hamshakan kasashe guda biyu, wato Mao Zedong da Julius Kambarage Nyerere wanda kuma sakamakon hakan, dangantakar ta ci gaba da samun bunkasuwa duk da canje-canje da aka samu na gwamnatoci.

Da kuma aka mar tambaya kan ziyarar shugaba Xi Jinping zuwa kasar Tanzaniya nan gaba, da kuma abin alherin da hakan zai haifar ga zumunci da kasar Sin da Tanzaniya suka kulla, jakadan ya ce, ba shakka irin wannan ziyara za ta kara dankon zumunci da aka riga aka kulla a baya.

Da kuma yake magana kan hadin gwiwa tsakanin kasar Tanzaniya da Sin karkashin sabuwar gwamnati, ya ce, suna burin samun ci gaba kamar yadda ya bayyana.

Jakada Biswaro na mai ganin taron BRICS da za'a yi ran 26 ga watan Maris a birnin Durban na kasar Afirka ta kudu a matsayin wata damar kara bunkasa hadin gwiwar kasashe masu tasowa.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China