in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane biyu sun rasu sakamakon wani hari a Tanzaniya
2013-05-07 12:35:54 cri

Rahotannin baya-bayan nan sun bayyana cewa, mutum na biyu ya rasu, sakamakon wasu raunuka da ya samu yayin harin bam da wasu, da ba a san ko su waye ba suka kai wata majami'ar Katolika dake Arusha ranar Lahadi 5 ga wata.

Mutumin na biyu ya rasu ne lokacin da ake kokarin kai shi wani asibiti dake Muhimbili, dake birnin Dar es Salam na kasar ta Tanzania.

Yayin da ya kai ziyarar gani da ido inda lamarin ya auku ranar Litinin, babban Sifeton 'yan sandan kasar Said Mwema ya ce, rundunar 'yan sandan kasar ta shiga farautar wadanda suka kitsa wannan danyen aiki. Ya ce, wannan aiki ne na wasu gungun mutane, ba wai mutum guda ba, don haka, za a dauki matakan da suka dace, domin damke dukkanin masu ruwa da tsaki a aukuwarsa.

Da yake tsokaci kan aukuwar harin, malamin majami'ar ta Arusha, Diocese Josephat Lebulu, cewa ya yi, bai taba ganin al'amari mai ta da hankali a cocin tasu makamancin wanda ya auku karshen makon da ya gabata ba. Ya ce, sun yi matukar kaduwa da jin karar fashewar, lokacin da suka fara ibada. Lebulu ya bayyana harin a matsayin wani mummunan laifi, duba da yadda ya sabbaba rasuwar wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, tare da jikkata wasu mutanen da dama.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China