Bankin bunkasa Afirka ADB ya amince da ba da rance kashi biyu, da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 232.5 don aikin ginin hanya mai tsawon kilomita 157.5 daga Arusha zuwa Holili a kasar Tanzaniya da kuma Taveta zuwa Voi a kasar Kenya.
Wata sanarwa daga bankin a yankin, da aka bayar a birnin Nairobi ranar Laraba na nuna cewa, wadannan kudade za su taimaka wajen rage farashin sufuri da kuma inganta samun amfanin gona, isa kasuwanni da ma sauran ababan bukatu na rayuwa tsakanin al'umomin gabashin Afirka.
Darektan bankin ADB na shiyya a cibiyar albarkatu ta gabashin Afirka, Gabriel Negatu ya ce, wannan hanya tana cikin takardar shirin dabarun dunkulewa na gabashin Afirka daga shekarar 2011 zuwa 2015, da na tsarin bunkasa sufuri a gabashin Afirka da kuma shirin bunkasa hanyoyi na yankin na watan Nuwamban shekarar 2011 a matsayin wata manufa ta sa hannu.
Negatu ya ce, al'umomin gabashin Afirka na kokarin bunkasa ababan sufuri don inganta shirin bunkasa tattalin arziki da zamantakewa a yankin, bunkasa harkokin shakatawa da kuma bunkasa niyyar dunkulewa, kana a samu raguwar kashe kudade kan harkar cinikayya ta hanyar ba da goyon baya ga harkar cinikayya tsakanin kan iyakoki da na kasa da kasa.(Lami)