in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu aikin kiyaye zaman lafiya na kasar Saliyo sun isa Somaliya
2013-04-04 09:49:03 cri

Dakarun aikin kiyaye zaman lafiya na kasar Saliyo sun isa kasar Somaliya ranar Laraba domin haduwa da sauran dakarun hadin gwiwa na kungiyar hadin kan kasashen Afirka dake aikin kiyaye zaman lafiya a Somaliya (AMISOM).

Wata sanarwa daga AMISOM na mai bayyana cewa, rukunin farko na dakarun Saliyo sun isa Somaliya jiya, kuma za su yi aiki tare da dakarun kasar Kenya.

AMISOM ta ci gaba da cewa, turo dakarun na Saliyo zai bai wa dakarun Kenya damar janye wasunsu daga yankin bisa tsarin kudurin kwamitin tsaro na MDD.

Sanarwar ta kara da cewa, wakilin musamman na maraba da turo dakarun tare da karin cewa, shigowarsu cikin dakarun AMISOM ya nuna dagewar da nahiyar Afirkan ta yi dangane da daidaita lamura a Somaliya.

Kasar Saliyo ita ce kasar Afirka ta biyar da ta ba da gudummawar dakaru ga rundunar kiyaye zaman lafiyan mai sojoji dubu 18 dake aikin kiyaye zaman lafiya a Somaliya tare da kasashen Uganda, Djibouti, Burundi, da kuma Kenya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China