in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kana hanyar soke majalisar dattawa a kasar Senegal
2012-08-30 10:19:53 cri

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya bayyana a kwanan nan a birnin Dakar cewa, ya dauki matakin mikawa majalisar dokokin kasarsa wata bukatar gaggawa na wani tsarin doka dake manufar soke majalisar dattawa. Matakin wata hanya ce ta kokarin rage kudaden da gwamnatin kasar take kashewa, ta yadda za'a samu damar maida hankali da tallafawa al'ummar kasar da ambaliyar ruwa ta shafa.

A cewar shugaba Sall, kudin da aka kebe domin aikin majalisar dattawa na Sefa biliyan takwas, za'a tura su a bangaren yaki da ambaliyar ruwa a kasar.

Amma duk haka shugaban kasar Senegal ya bayyana cewa, za'a cigaba da tattaunawa kan wannan batu tare da sauran jam'iyyun siyasa na kasar a nan gaba domin samar da hanyoyi da sharudan da suka wajaba wajen sake kafa wata majalisar dattawa da za ta zo daidai da halin da kasa take ciki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China