in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci shugabannin Afrika da su taimaka wajen rage mutuwar kananan yara
2013-05-09 10:59:28 cri

Fiye da jarirai miliyan guda suke mutuwa ranar haifuwarsu a kowace shekara, lamarin da ya mai da kasashen Afrika dake kudu da Sahara a matsayin yanki mafi hadari wajen haifuwa, a cewar wani rahoto na kungiyar ceton kananan yara.

Rahoto na 14 na wannan kungiyar kan halin mata a duniya ya nuna cewa, shiyyar Afrika dake kudu da hamadar Sahara na da adadin mutuwa wajen haifuwa mafi girma, cewa mace daya cikin mata 31 na mutuwa bisa dalilin juna biyu. A kasashen da suka samu cigaban masana'antu kuwa, wannan hadari yana bisa mace daya cikin 4300.

A cewar wannan rahoto, kasashen DRC-Congo, Mali, Sierra Leone da Somaliya suna da adadin mutuwar kananan yara mafi girma a duniya.

Ya kamata gwamnatocin Afrika da gamayyar kasa da kasa su rika aiki tare domin kawo karshen halin da ake ciki yanzu idan ana son cimma wannan babban buri, haka kuma a mai da hankali wajen kare jarirai a cikin ranar farko da watan farko na rayuwarsu, in ji Hussein Halane, darektan shiyya na kungiyar ceton kananan yara "Save the children" a gabashin Afrika.

Mista Halane ya kara da cewa, za'a iyar ceton yawan yara daga mutuwa idan ana aiwatar da matakan aiki masu nagarta.

MDD ta bayyana cewa, adadin mutuwar uwa da jinjirinta ya karu tsakanin shekarar 1990 da ta 2008. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China