in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Albarkatun kasa su ne tushen tashin hankali a Afrika, in ji babban jami'in tsaron AU
2013-05-06 12:38:37 cri

Wani babban jami'in tsaro na kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU a jiya Lahadi 5 ga wata ya ce, albarkatun kasa za su iya zama albarka da kuma masifa dake da alaka da yawan tashin hankali a Afrika.

Kwamishinan wanzar da zaman lafiya da tsaro Ramtane Lamamra ya sheda ma manema labarai a lokacin taro karo na 10 na kungiyar liken asiri da tsaro na nahiyar Afrika da aka yi a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe cewa, albarkatun kasa su ne suka fi yawo hankali masu saka ma nahiyar ido daga kasashen waje.

Ya ce, 'Idan aka duba da kyau, kowane tashin hankali dake wanzuwa a nahiyar za'a ga cewar, babban dalilin shi ne albarkatun kasa, ko dalilin ya zama a bayyane ko kuma a boye."

Don haka, in ji shi, akwai bukatar nahiyar Afrika ta bullo da wassu dabaru don amfana da wadannan albarkatun kasa, ta yadda za su zama alheri ga mazauna wurin da suke.

Ita dai kungiyar liken asiri da sa ido na Afrika, CISSA, an kafa ta ne a shekara ta 2004 sakamakon bukatar hakan da shugabannin kasashen nahiyar suka gabatar na son a samar da bayanai na sirri da ya shafi nahiyar, kuma wani bangare ne na kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU dake da alhakin samar da bayanan tsaro ga nahiyar.

Jigon taron wannan shekarar dai a taron da za'a kammala ranar 8 ga wata shi ne "samar da hanyoyin amfani tsakanin albakatun kasa a Afrika, cigaba da tsaro."

Kafar yada labaran kasar Zimbabwe ta ce, ana sa ran shugaban kasar Zimbabwe Robert Mogabe da shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU Dr. Nkosazana Dlamini Zuma za su halarci taron wanda abin da aka zartar a lokacin za'a gabatar da shi ga shugabannin kasashe a taron AU mai zuwa.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China