Kungiyar tarayyar kasashen Afrika (AU), kungiyar cimaka da noma ta majalisar dunkin duniya (FAO) sun gudanar a kwanan nan a birnin Addis Abeba na kasar Habasha da wani zaman taro kafin babban taro na manyan jami'ai kan kokarin da suka shafi kawar da yunwa a nahiyar Afrika.
Tare da hadin gwiwar kungiyar FAO, sabon tsarin hadin gwiwa domin cigaban Afrika (NEPAD), kungiyar AU za ta shirya wani babban taro na manyan jami'ai a cikin watan Yuni domin duduba hanyoyin da za'a bi wajen gaggauta kokarin da ya shafi kawar da bala'in yunwa a nahiyar Afrika.
Darektan kula da cigaban karkara da noma na kungiyar AU, mista Abebe Haile-Gebriel ya nuna cewa, ko shakka babu, akwai damar kawar da yunwa a Afrika, tare kuma da yin amfani da wannan dama wajen kira da a gaggauta ayyukan cimma wannan buri ta hanyar amfani da yawan hanyoyi da dabaru da ake da su a Afrika.
Tare da bayyana cewa, ya kamata a nan gaba a cimma wani shirin dake kunshe da nagartattun ayyuka domin daidaita tsare-tsaren da ake aiwatarwa na kawar da yunwa a nahiyar Afrika. (Maman Ada)