in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 15 sun rasu a Damascus dake Syria sakamakaon harin kunar bakin wake
2013-04-09 13:31:19 cri

A kalla mutane 15 sun rasa rayukansu yayin da wasu 53 suka samu rauni ranar Litinin, bayan da wata mota dake dankare da ababan fashewa ta tashi a tsakiyar Damascus, babban birnin kasar Syria, in ji wani da abin ya auku a idonsa.

Dan kunar bakin waken ya kai hari ne a wajen ajiye motoci na babban bankin kasar Syria, inda ya yi sanadin salwantar rayukan mutane 15.

Babu wanda ya dau alhakin wannan hari, to amma harin yana da kamanni da wadanda kungiyar Al-Qaida ta kai a baya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China