Yau Laraba 8 ga wata da safe, shugaban kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya iso nan birnin Beijing bayan ziyarar da ya kai a birnin Shanghai a ci gaba da ziyarar da yake a kasar Sin na tsawon kwanaki biyar.
Yayin ziyarar tasa, shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan kasar Li Keqiang za su gana da Benjamin Netanyahu, wadda ta kasance sabuwar ziyararsa ke nan a nan kasar Sin bayan wacce ya yi shekaru shida da suka gabata, wadda kuma ta zamo karo na farko da shugabannin kasashen biyu suke ganawa tun bayan da Sin ta zabi sabbin shugabanni a watan Maris na bana.
Kafin ziyarar tasa, Benjamin Netanyahu ya nuna cewa, wani muhimmin abu da za a tattauna a kai shi ne batun kara fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin. Mutane masu yawa ne ke yi wa Benjamin Netanyahu rakiya, ciki hadda manyan jami'ai masu kula da harkokin tattalin arziki da cinikayya da kuma 'yan kasuwa.
Kasashen biyu za su daddale wasu yarjeniyoyi dangane da hadin gwiwa tsakaninsu yayin ganawar. (Amina)