in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotu za ta dubi yiwuwar ba da belin tsohon shugaban kasar Masar
2013-04-15 13:00:10 cri

A yau Litinin ne wata kotu a Masar, za ta duba bukatar da aka gabatar mata, na ba da belin tsohon shugabn kasar Hosni Mubarak, kamar dai yadda kamfanin dillanci labarun kasar MENA ya rawaito.

Lauyan Mubarak Farid Al-Deeb ne dai ya gabatar wa kotun wannan bukata, yana mai cewa, tsohon shugaban mai shekaru 84 da haihuwa, ya haura tsahon lokacin tsaro na wucin gadi da doka ta tanada. Yayin zantawarsa da wakilin kamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xinhua, lauyan na Mubarak ya ce, shekaru 2 da ake iya tsare wanda ya ke karewa kafin yanke masa hukunci, sun cika a ranar 12 ga watan nan, don haka ya zama wajibi a ba da belin tsohon shugaban a yanzu.

An dai cafke tsohon shugaba Mubarak ne a watan Afrilun shekarar 2011, sakamakon zarginsa da aka yi da ba da umarnin kisan masu zanga-zanga a cikin watan Janairun wannan shekara, aka kuma yanke masa hukuncin daurin rai da rai a watan Yunin shekarar 2012. A kuma watan Janairun shekarar 2013, wata kotun daukaka kara ta ba da umarnin sake shari'ar da aka gudanar, sakamakon rashin bin ka'idoji da ta ce an yi yayin tsohuwar shari'ar. A kuma ranar Asabar din da ta gabata ne aka dage shari'ar baki daya, sakamakon janyewar da alkalin da ke gudanar da shari'ar Mustapha Hassan Abdullahi ya yi, inda ya mika shari'ar ga kotun daukaka kara a karo na biyu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China