Kungiyar tsagerun yankin Niger Delta dake kudu maso kudancin Najeriya ko MEND a takaice, ta ce, tun daga wata mai zuwa, za ta fara kai hare-hare kan cibiyoyin mabiya addinin musulunci dake kasar.
Cikin sanarwar da kungiyar ta fitar ga manema labaru ta hanyar sakon karta kwana a ranar Lahadi 14 ga watan nan, ta ce za ta dauki wannan mataki ne domin ramuwar kisan da kungiyar nan ta Boko Haram, ke yi wa Kiristoci ba ji ba gani. Hare-haren da MEND din ta ce, za ta kaddamar masu lakabin "Operation Barbarossa", za su mai da hankali ne kan masallatai, da sansanonin masu niyyar zuwa aikin hajji, da wuraren tarukan musulmi, da kuma kisan malaman addini masu bayyana tsattsauran ra'ayi.
Sanarwar da kakakin kungiyar ta MEND Jomo Gbomo ya fitar ta kara da cewa, za su yi amfani da bama-bamai, a matsayin babbar hanyar daukar wannan mataki da suka ayyana. Sai dai Gbomo ya ce, za su iya dakatar da wannan kuduri nasu idan har kungiyar Kirista, da malaman majami'u na hakika suka tabbatar da daina kai hare-hare, da kungiyar ta Boko Haram ke aiwatarwa, tare da samun tabbas a bayyane, daga ainihin jagororin kungiyar ta Boko Haram.
An dai fara jin duriyar kungiyar ta MEND ne a Najeriya, tun cikin shekarar 2006, lokacin da ta fara gwagwarmayar samun yancin yankin Niger Delta mai arzikin man fetir, bayan da ta bayyana wa duniya cewa, talakawan Niger Deltan ba sa morar arzikin da Allah ya huwace wa yankin, don haka za su dauki matakin sauya lamarin.(Saminu)