Rahotanni daga kasar Libya sun bayyana aukuwar wani yunkuri na kisan Jala Al-Regi, wanda ke matsayin kwamandan bataliyar babban kwamitin tsaron kasar, da yammacin ranar Laraba 27 ga watan nan.
Harin wanda ake zaton na ramuwar gayya ne, ya faru ne a yankin Tajoora, yanki mafi girma dake wajen babban birnin kasar wato Tripoli. Maharin dai ya tsere bayan yunkurin kisan Al-Regi, ko da yake dai hakarsa bai cimma ruwa ba.
Bisa labarin da aka samu, an ce, kafar Al-Regi ta samu rauni sakamakon harbin bindiga har guda 5, inda a yanzu haka yake asibiti domin samun kulawar likitoci. Tuni kuma jami'an tsaro suka fara gudanar da bincike kan aukuwar wannan lamari.(Saminu)