Masu gani da ido sun bayyanawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewa, wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kutsa cikin ginin gidan talibijin din Al-Assema dake Libya ranar Alhamis, suka kuma yi awun gaba da mutane 4.
Daruruwan 'yan bindiga ne suka kaiwa gidan talibijin din farmaki a yankin Gorji kusa da Tripoli inda suka lalata kayayyaki, in ji Rajab Ben Gazi wanda abin ya auku a idonsa.
An sace mutane 4, ciki har da manajan gidan talibijin din Juma Usata, in ji wanda ya ga lamarin, ya kuma kara da cewa, 'yan bindigar suna zargin Usata da cewa, yana goyon bayan Muammar Gaddafi, suka kuma zargi gidan talibijin din da cewa, yana da alaka da kungiyar dakarun hadin gwiwa ta kasar karkashin jagorancin Mahmoud Jibril.
Jami'an tsaro sun dauki karin matakan tsaro a yankin tare kuma da tantance abin da aka lalata.
An saki daya daga cikin wadanda aka sace, Mahmoud Sharkisi inda ya ce, 'yan bindigar sun mutunta shi.(Lami)