in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a kafa dokar hana fita a Benghazi in ya zama dole, in ji firaministan Libya
2013-01-17 10:00:37 cri

Firaministan kasar Libya Ali Zeidan a Laraban nan 16 ga wata ya ce, gwamnatinsa da babban taro na kasa za su yi nazarin kafa dokar hana fitar dare a Benghazi in har ya zama dole saboda yanayin birnin a 'yan kwanakin nan ba shi da kyau.

Firaministan wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ya ce, suna tattaunawa game da yiwuwan dokar a Benghazi da ma wasu garuruwa, sai dai kuma ba'a tsai da shawarar ba tukun nan a kan kasancewar shi rabi da rabi wanda zai shafi wasu wurare kawai, amma lallai akwai yiwuwan hakan.

Zeidan ya kara da cewa, gwamnati za ta yi iyakacin kokarinta na ganin cewa, Benghazi ya samu kariyar da ya kamata, kuma ba'a kafa rundunar kariyar diflomasiya ba tukun na kuma ba za'a mai da garin wani sansanin soja ba tukun a yanzu, amma za'a yi yunkurin saka dokar hana fitar dare har sai yanayin tsaro ya inganta.

Yawan hare-haren da ake kai wa jami'an soji da 'yan sanda da suka hada da wadanda suka yi aiki da tsohon gwamnati ya karu kwarai a cikin 'yan makwannin nan, duk da kokarin sabon gwamnati wajen ganin ta inganta sha'anin tsaro.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China