Gwamnatin Siriya ta amince da nadin Ake Sellstrom, kwararre daga kasar Sweden, a matsayin jagoran tawagar binciken ta M.D.D., da sakataren janar na majalisar Ban ki-moon ya yi. Nesirky ya jaddada cewa, dalilin da ya sa za a gudanar da wannan bincike shi ne, don tabbatar da ko akwai makamai masu guba a kasar ko kuwa a'a.
Ban da wannan kuma, an ce, membobin tawagar binciken sun hada da kwararru na hukumar hana yaduwar makaman kare dangi, da na kungiyar kiwon lafiya ta duniya. Haka kuma, Nesirky ya sake jaddada cewa, kamar yadda Ban Ki-moon ya fada, tawagar binciken ta bukaci da a gudanar da aiki cikin 'yanci.
Bisa labarin da aka sanya a kan shafin Internet na M.D.D., an ce, Sellstrom da aka nada a matsayin jagoran tawagar binciken, ya ce, zai fara gudanar da wannan aiki cikin mako mai zuwa.(Bako)