in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban bangaren 'yan adawa na kasar Siriya Khatib ya sanar da yin murabus
2013-03-25 10:12:02 cri
A ran 24 ga wata, shugaban bangaren 'yan adawa na kasar Siriya NCSROF Mouaz Al-Khatib ya yi murabus daga mukaminsa a birnin Alkahira hedkwatar kasar Masar.

Al-Khatib ya bayyana a shafin Twitter cewa, ya taba yi wa jama'ar Siriya alkawari cewa, idan wasu abubuwan da aka yi sun wuce "iyakar da aka zana", zai yi murabus. Amma bai bayyana hakikanin abun da ya mai da shi yin murabus ba.

Amma duk da haka, Al-Khatib ya bayyana cewa, zai ci gaba da dukufa ka'in da na'in game da batun makomar kasar Siriya, to, sai dai manazarta sun bayyana cewa, dalilin da ya sa Al-Khatib ya yi murabus shi ne kasashen duniya na nuna sakaici game da rikicin zub da jini a kasar Siriya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China