Ya zuwa yanzu, an tabbatar da mutane 129 da suka kamu da cutar murar tsuntsaye, cikinsu mutane 31 sun mutu, kuma mutane 42 sun wartsake.
A ranar 6 ga wata, hukumar kula da kiwon lafiya da tsara shirin haihuwa ta bayar da labari a shafinta na Internet cewa, kwanan baya, mujallar kimiyya ta Birtaniya "Nature" ta yi bayani cewa, gwamnatin Sin ta dauki kwararan matakai cikin hanzari don yaki da cutar murar tsuntsaye, don haka wajibi ne a jinjina kokarin gwamnatin Sin wajen bayar da rahoto da labaru a bayyane.(Bako)