in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomin M.D.D. da dama sun yaba wa kokarin da kasar Sin ta yi wajen yaki da cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9
2013-04-12 15:28:48 cri
Kwanan baya, hukumomin M.D.D. da kungiyoyin kasa da kasa sun nuna yabo da goyon baya game da kokarin da kasar Sin ke yi wajen yaki da cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9, kuma sun bayyana cewa, Sin ta kokarta wajen yaki da wannan cuta cikin hanzari kuma a bayyane.

Cibiyar yada labaru ta M.D.D. ta bayyana cewa, M.D.D. ta nuna yabo game da kasar Sin, sabo da ta gabatar da bayanai kan mutanen da suka kamu da cutar cikin lokaci, da bayar da labaru dala-dala ga jama'a kan cutar da matakan yin rigakafi.

A ranar 11 ga wata, hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ci gaba da jinjinawa tare da nuna goyon baya ga kokarin da kasar Sin ke yi wajen yaki da cutar, kuma a cewarta, ya zuwa yanzu, ba a gano cikakkun shaidu cewa, an samu yaduwar cutar tsakanin jama'a ba, sannan, hukumar ta ba da shawarar hana kafa wuraren bincike na musamman a hukumomin kwastam na kasar, balle ma hana tafiye-tafiye da yin cinikayya tsakanin Sin da kasashen duniya.

A ranar 11 ga wata, kungiyar kiwon lafiyar dabbobi ta duniya OIE ita ma, ta ba da sanarwa, inda ta jaddada cewa, kamata ya yi a inganta hadin gwiwa da ke tsakaninta da kasar Sin, don yaki da sabon kalubalen da aka samu wajen yaki da cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9.

A ranar 11 ga wata, hukumar kula da harkokin tsara shirin abinci da aikin gona ta M.D.D. ta shirya wani taron manema labaru a birnin Bangkok da ke kasar Thailand, inda ta bayyana halin da ake ciki wajen yaki da cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9. Direktan sashen daidaita batun yaki da cututtukan dabbobi cikin gaggawa na hukumar Subhash Morzaria ya bayyana cewa, gwamnatin Sin ta ba da bayanai kan yadda take yaki da cutar ga kasashen duniya cikin lokaci kuma a bayyane, kuma ta tashi tsaye don yin hadin gwiwa da kasashen duniya, don hana yaduwar cututtuka.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China