Daga ranar 13 ga wata da karfe 5 na yamma zuwa ranar 14 ga wata da karfe 5 na yamma, an samun karin mutane 11 da suka kamu da wannan cuta, kuma 2 daga cikinsu sun mutu a birnin Shanghai.
Ya zuwa yanzu, an samu mutanen da suka kamu da cutar a biranen Beijing da Shanghai, da lardunan Jiangsu da Zhejiang, da sauran larduna 2 na kasar.
Haka kuma, an yi nazari ga mutanen da suka yi mu'amala sosai da wadannan mutane masu dauke da cutar, amma ba a gano alamun samun yaduwar cutar tsakanin mutane ba, sai dai ya zuwa yanzu, wannan cuta na ta ci gaba da yaduwa a sassan kasar ta Sin.(Bako)