in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Amurka ta kasance kwarya mai baki biyu kan batun kare hakkin dan Adam na kasar Sin
2013-04-22 20:15:50 cri
Game da rahoton da ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka ta fitar a kwanan baya kan halin da kasashen duniya suke ciki a game da harkokin kare hakkin dan Adam na shekarar 2012 a ranar 19 ga wata, inda aka sake zargi halin kare hakkin dan Adam na kasar Sin, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a nan birnin Beijing a ranar 22 ga wata cewa, rahoton da kasar Amurka ta gabatar bai dace da hakikanin halin kare dan Adam na duniya ba, kana ta kasance kwarya mai baki biyu kan batun kare hakkin dan Adam a tsakaninta da sauran kasashen duniya.

Hua Chunying ta kara da cewa, babu wata kasa a duniya maras aibi a harkokin kare hakkin dan Adam. Kasar Sin tana son yin mu'amala tare da sauran kasashen duniya kan wannan batu bisa adalci da girmama juna, don kara fahimtar juna da inganta aikin kare hakkin dan Adam. Amma Sin ba ta amince da yin amfani da batun kare hakkin dan Adam wajen tsoma baki kan harkokin cikin gida na wata kasa ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China