'Yan sandan birnin Boston dake kasar Amurka sun bayyana a daren ranar 19 ga wata cewa, an riga an kama mutumin da ake zarginsa da laifin ta da boma-bomai a wajen gasar ya-da-kanen-wani da akayi a birnin, inda yanzu kuma ana ci gaba da bincike kan yankin da ake ciki.
A wancan rana jami'an tsaro sun yi samame a karkarar birnin Boston, inda suka yi musayar wuta da mutanen 2 da ake zarginsu da laifin kai wannan farmaki. Ya zuwa daren ranar, an gano daya daga cikin mutanen 2, Dzhokar Tsarnaev, da ke da shekaru 19 da haihuwa, cikin wani kwale-kwale. Sa'an nan aka yi masa kawanya, aka kama shi.
Kafofin watsa labarun kasar Amurka sun ce Dzhokar din ya ji rauni, don haka an kai shi asibiti. Kana dayan mutumin da ake zargi da laifi, kuma wan Dzhokar, Tamerlan Tsarnaev mai shekaru 26 a duniya, ya riga ya mutu yayin musayar wuta da suka yi da 'yan sanda a daren ranar 18 ga wata.
A yammacin ranar 15 ga wata, an samu tashin jerin boma-bomai a wajen wata gasar ya-da-kanen-wani ta kasa da kasa da ta gudana a birnin Boston,inda lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 3, da jikkatar da wasu fiye da 170. (Bello Wang)