A cikin wata sanarwar da fadar shugaban kasar Amurka wato White House ta fitar, an ce, manyan jami'an da suka halarci taron kwamitin tsaron kasar na mintoci 90 sun hada da mai bada taimako kan harkokin tsaron kasa, mai bada taimako ga shugaban kasar Amurka mai kula da harkokin tsaron yankunan kasar da yaki da ta'addanci, ministan tsaron yankunan kasar, shugaban hukumar binciken manyan laifuffuka ta kasar, da kuma ministan mai kula da harkokin shari'a na kasar. Kana mataimakin shugaban kasar Amurka Joseph Biden ya halarci taron ta hanyar wayar tarho mai telebijin. Shugaba Obama ya bukaci hukumomin da abin ya shafa da su kara yin bincike kan lamarin don gano dalilin faruwarsa.
Boma-bomai sun fashe ne a birnin Boston yayin da ake gudanar da gasar gudun yada-kanin-wani, inda suka haddasa mutuwar mutane 3, yayin da kuma mutane fiye da 170 suka ji rauni. Wannan ne harin ta'addanci mafi tsanani tun bayan harin birnin New York da aka kai a ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2011 a kasar ta Amurka. (Zainab)