in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun yi Allah wadai da fashewar boma-bomai a kasar Amurka
2013-04-17 10:27:24 cri

An samu fashewar boma-bomai, yayin da ake gudanar da gasar gudun yada-kanin-wani a birnin Boston dake kasar Amurka a ranar 15 ga wata, wadanda suka haddasa mutuwar mutane 3, da kuma jikkata mutane fiye da dari. Lamarin da daukacin kasashen duniya suka yi Allah wadai da shi.

A ranar 16 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya buga waya ga shugaban kasar Amurka Barack Obama, inda ya jajantawa gwamnatin kasar Amurkan, da jama'arta sakamakon faruwar lamarin na fashewar boma-bomai a birnin Boston.

Shugabannin kasashen Rasha, Koriya ta kudu, da Jamus, da sauran kasashen duniya su ma sun yi tir da wannan lamari.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China