Darektar yammacin Afirka ta sashen kula da harkokin tattalin arziki da rage talauci ta bankin duniya, madam Miria Pigato ta sanar a ranar Laraba a birnin Dakar cewa, "akwai rashin daidaito" a fuskar kashin kudin gwamnati a kasar Senegal, musmaman a wasu bangarorin masana'antun kasar.
A lokacin da take jawabi a yayin wani taron kara wa juna sani, madam Pigato ta yi kira ga hukumomin kasar Senegal da su daidaita wannan matsala ta yadda kashin kudin gwamnati zai kasance bisa daidaici inda ta ce, akwai "tattatuwar kasha-kashen kudin gwamnati a yankin Dakar kawai."
Hakazalika, ta bayyana cewa, manufar ba da tallafin gwamnatin kasar Senegal ta kasance wata hanyar dake kawo rauna ga daidaituwar kashin kudin gwamnatin.(Maman Ada)