Thiam ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da aka bayar a Dakar, babban birnin kasar biyo bayan rade-radin da wasu na hannun daman shugaban ke yi cewa,mai yiwuwa ba zai iya rage tsawon wa'adin mulkinsa ba, kana 'yan adawa suma suna shakku game da gaskiyar shugaban kan wannan batu.
Kakakin shugaban ya fada cewa, "shugaba Macky Sall a yau da kuma kowane lokaci, a shirye ya ke ya cika alkawarin da ya yiwa 'yan kasarsa. Daga cikin wadannan alkawura,har da rage tsawon wa'adin mulkin shugaban kasa wanda ya sake nanatawa a ranar 3 ga watan Afrilu.
Idan za a iya tunawa, a wannan lokaci ne Sall ya tabbatar da cewa, ya yanke shawarar rage tsawon wa'adin mulkin shugaban kasa daga shekaru 7 zuwa 5. (Ibrahim)