in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya yi kira ga kasashen duniya da su taimaka wa kasashen da rikicin ya shafa wajen aikin sake yin gine-gine cikin lumana
2013-04-26 16:09:58 cri
A ranar 25 ga wata, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin da ke M.D.D. Wang Min ya bayyana cewa, lokacin da kasashen duniya suka taimaka wa wasu kasashen da rikicin ya shafa wajen sake gina su cikin lumana, kamata ya yi a mayar da batun girmama mulkin kansu ya zama babbar ka'idar da za a bi, sannan a taimaka musu wajen tsara manyan tsare-tsare na samun bunkasuwa cikin lumana bisa halin da ake ciki a kasashensu.

A wannan rana, kwamitin sulhu na M.D.D. ya shirya taro game da sake gina kasashe cikin lumana bayan rikici. A jawabinsa, Wang Min ya ce, bayan da aka sassanta rikici a wasu kasashe, ya zama wajibi wadannan kasashe su dauki alhakin bisa wuyansu wajen saka gina kasashe cikin lumana, kuma ya kamata kasashen duniya su mutunta anniyarsu da mulkin kansu, su ba da taimako na a zo a gani a fannonin da gwamnatocin wadannan kasashe suka tsayar.

Haka kuma, Wang Min ya yi nuni cewa, a cikin wani dogon lokacin da ya gabata, bayan da aka samu rikici a wasu kasashe, kasashen duniya ba su sa kulawa sosai ba game da samun bukasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma na wadannan kasashe a yunkurinsu na sake yin gine-gine bayan rikici, har ila yau ya yi kira ga kasashen duniya da su samar da hakikanin taimako, ba tare da gindaya wasu sharudda ba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China