in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya yi kiran a kawo karshen matsalar da mutane ke ciki a Sudan
2013-04-19 10:16:10 cri

Zaunannen wakili kuma jami'in gudanar da ayyukan jin kan bil-adama na MDD a kasar Sudan Ali Al-Za'tari, a ranar Alhamis ya yi kiran a kawo karshen rikici a kasar, da ya yi sanadin kaurar mutane sama da miliyan daya yayin da sama da mutane dubu dari biyu sun fice daga kasar, in ji mai magana da yawun magatakardan MDD yayin jawabi ga manema labaru.

Martin Nesirky wanda shi ne mai magana da yawun magatakardan MDD Ban Ki-Moon, yayin bayani da aka saba yi kullum ya bayyana cewa, sama da mutane miliyan daya sun kaura ko sun bar muhallinsu, sannan sama da dubu dari biyu sun fice daga kasar zuwa kasashe dake makwabtaka da ita.

Bugu da kari, akwai matsalar ceton bil-adama a gabashin yankin Darfur, in ji wakilin musamman na hadin gwiwar aikin kawo zaman lafiya a Sudan na kungiyar hada kan kasashen Afirka da MDD a Darfur, (UNAMID), Mohammed Ibn Chambas.

Nesirky ya ci gaba da cewa, Chambas ya gana da ministan harkokin cikin gida na kasar Sudan Ibrahim Mahmoud Hamed ranar Laraba, dangane da yanayin jin kan bil adama a garuruwan Labado da Muhajeria dake gabashin yankin Darfur, inda ya bukaci gwamnati ta tabbatar da cewa, masu ba da kayayyakin agaji na samun isa wadannan yankuna.

'Yan tawaye a Darfur sun rarrabu zuwa kungiyoyi daban daban tun lokacin da suka fara ta da kayar baya a shekarar 2003 inda hakan ke gurguntar da yunkurin kafa zaman lafiya da karin tabarbarewar tsaro a yammacin kasar Sudan, kana rayuka sama da dubu dari uku sun salwanta sakamakon rikicin, in ji MDD.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China