Yau Jumma'a ranar 26 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin CPPCC Yu Zhengsheng ya gana da shugaban majalisa mai kula da harkokin tattalin arziki da al'ummar kasar Mauritaniya Mohamed Ould Haimer.
A yayin ganawar, Yu Zhengsheng ya ce, a cikin shekaru 48 da kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, Sin da Mauritaniya sun tafiyar da dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata, tare kuma da samun ci gaba mai kyau a fannoni daban-daban dangane da yin hadin gwiwa. Kasar Sin ta yabawa goyon baya da Mauritaniya ke yi mata a kan wasu manyan batutuwan da suka hada da batun yankin Taiwan, jihar Tibet, jihar Xinjiang da hakkin Bil Adam da sauransu. Don haka majalisar CPPCC na fatan kara yin hadin gwiwa ta bangarori daban-daban ciki hadda majalisar tattalin arziki da al'immar Mauritaniya domin ci gaba da yin mu'amala a dukkan fannoni, da ciyar da dangantakarsu ta sada zumunci gaba.
A nasa bangare, Mohamed Ould Haimer ya nuna juyayi sosai ga mutanen da suke fama da girgizar kasa a lardin Sichuan. Sannan kuma ya nuna godiya ga taimakon da gwamnatin kasar Sin ke baiwa kasar sa a fannin tattalin arziki da zaman al'umma cikin dogon lokaci, har ma ya yi fatan samun karin hadin gwiwa tsakanin majalisun kasashen biyu ta yadda za a ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba. (Amina)