'Harbi ne da aka kai bisa kuskure kan ayarin motocin shugaban kasar a yayin da yake dawowa daga wani rangadin aiki a cikin kasar, wadannan sojoji basu san cewa ayarin shugaban kasa ba ne, kuma harbi ne na yin kashedi da wani rukunin sojojin dake sintiri a Tweira dake arewacin hanyar shigowa birnin Nouakchott suka yi' in minista Ould Mahjoub.
Haka kuma ya kara da cewa mutanen kasar Mauritania su kwantar da hankalinsu, domin shugaban kasar na cikin koshin lafiya kuma yana samun jinya a asibitin soja, duk da cewa shugaban Adel Aziz ya samu dan rauni, amma da kansa ya sauko daga cikin mota ba tare da wata matsala ba.
Sai dai da farko, wata majiyar jami'an tsaro ta bayyana cewa wasu mutanen da ba'a da masaniya kansu suka kai wannan hari.
Dan asalin Inchiri dake arewacin birnin Nouakchott, shugaban kasar Mauritania na zuwa lokaci zuwa lokaci a wannan yankin a lokacin hutun mako.
Kuma tun yau da 'yan kwanaki ne, jami'an tsaron kasar suke gudanar da bincike kan mutane da motoci a wajen hanyoyin dake hadewa da babban birnin kasar.
A cewar wata majiyar soja data bukaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa matukin motar da shugaban kasar yake ciki bai bi umurnin gargadin da aka yi masa ba, dalilin da ya sanya sojojin suka kai harbi kan wannan ayari.
Daga bisani kuma aka samu musayar wuta tsakanin wadannan sojojin dake sintiri da sojojin dake tsaron lafiyar shugaban kasar, a lokacin ne shugaba Abdel Aziz ya samu karamin rauni a cewar wannan majiya.
Ould Abdel Aziz na kan karagar mulki tun a shekarar 2008, bayan wani juyin mulkin da ya hambarar da shugaba Sidi Ould Chiekh Abdallahi. Bayan da aka cimma wata yarjejeniya tsakanin jam'iyyun siyasa na kasar a birnin Dakar na kasar Senegal, Ould Abdel Aziz ya yi murabus daga rundunar sojojin kasar a cikin watan Yunin shekarar 2009 domin shiga takarar zaben shugaban kasa inda kuma ya lashe wannan zabe da samun kuri'un kashi fiye de 52 cikin 100.
A wani labari na daban da muka samu, an ce an isa da shugaban kasar Mauritania a ranar yau Lahadi da safe zuwa kasar Faransa domin samun jinya a cikin wani jirgin sama na musammun da gwamnatin kasar Faransa ta tura zuwa kasar MauritaniaKafin tashinsa zuwa kasar Faransa, shugaban Mohamed Ould Abdel Aziz ya yi wani jawabi ta kafofin rediyo da talabijin na kasar domin yin kira ga mutanen kasar da su kwantar da hankalinsu da kuma neman zaman lafiya ga kasar.(Maman Ada)