Bisa rahoton da kungiyar kula da kiwon lafiyar duniya ta bayar, an ce, ma'aikatar kiwon lafiya ta Mauritania da ma'aikatar bunkasa karkara ta kasar, sun riga sun aike da wata kungiyar bincike zuwa yankin da ake fama da wannan cuta.
Bugu da kari, a ran 3 ga watan, kungiyar kiwon lafiyar duniya da hukumar samar da abinci da aikin gona ta MDD za su tura masana zuwa yankin don sa ido kan ayyukan samar da agaji, da kuma fadakar da mazaunan wurin masu kiwon dabbobi kan matakan rigakafin cutar da na shawo kanta.
A shekarar 2010, an taba samun barkewar annobar zazzabin "Rift Valley" da dabbobi ke yadawa a Mauritania. Mutane da dabbobi suna iya kamuwa da wannan cutar sakamakon wasu nau'o'in kwayoyin cuta, musamman ma dabbobi kamar shanu, tumaki da rakuma da dai sauransu sun fi saukin kamuwa, kuma 'yan Adam na iya daukar wannan cuta ta hanyar shan madara ko taba jini ko sassan jikin dabbobin da suka kamu da cutar, haka kuma sauro na yada cutar. (Maryam)