A yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jaridar TV5 Monde da RFI, shugaba Ould Abdel Aziz ya nuna cewa, dukkan abubuwa sun hadu kuma suna nan domin maida kasar Mali wata Afghanistan.
Shugaban Mauritaniya ya bayyana cewa, matakin da gwamnatin tsakiya ta Mali ta dauka na yin watsi da arewacin kasar ya janyo matsalolin ta'adanci da sumogal sun yi kanta a yankin.
Haka kuma ya yi watsi da sanarwar kafa wata sabuwar kasa a cikin yankin arewacin Mali, "wannan ya rataya ga mutanen kasar Mali na yanke shawarar amincewa ko a'a game da baiwa arewacin Mali cin gashin kansa. Ba za mu nuna adawa ba idan har 'yan kasar Mali suka amince da haka", in ji shugaban kasar Mauritaniya.
Hakazalika mista Ould Abdel Aziz ya yi watsi da ra'ayin yin shawarwari tare da mayakan 'yan kishin islama dake arewacin kasar Mali. (Maman Ada)