in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kudin cinikin da Sin da Mauritaniya suka samu ya kai matsayin koli
2012-02-20 10:46:51 cri

Ma'aikatar kwastan kasar Sin ta ba da kididdiga cewa, a cikin shekarar 2011, yawan kudin da Sin da Mauritaniya suka samu a fannin ciniki ya kai dala miliyan 1925 wanda ya karu da kashi 53 cikin 100 bisa na makamancin lokaci na shekarar 2010, daga cikinsu, yawan kudin da Sin ta kashe wajen shigo da kayayyaki daga Mauritaniya ya kai dala miliyan 1500 wanda ya karu da kashi 58 cikin 100 bisa na makamancin lokaci na shekarar 2010. Jimillar karuwar da Sin ta samu sun haura ta wadanda Sin da kasashen Afrika suka samu a wannan fanni a shekarar 2011.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, wasu ma'addinai kamar karfen tama da tagulla sun kasance muhimman kayayyaki da Sin ta shigo da su daga kasar Mauritaniya. Ya zuwa yanzu, Mauritaniya ta kasance kasa mafi girma da ta samarwa kasar Sin karfen tama a naihiyar Afrika. Saboda farashin karfen tama na kan matsayin karuwa, hakan ya sa, yawan kudin da Sin ta kashe wajen shigo da karfen tama ya karu sosai. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China