An kama masu gwagwarmayar yaki da bauta biyar a Mauritaniya
Wasu masu gwagwarmayar yaki da bauta su biyar dake cikin kungiyar masu neman kawar da cin zarafin dan adam (IRA) na cikin hannun hukumomin kasar Mauritaniya tun a ranar Asabar a birnin Nouakchott, an kama su a yayin da suke halartar wata zanga-zanga ta neman a sako shugaban kungiyar IRA, a wani labari da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu daga wasu kungiyoyin fararen hula na kasar ta Mauritaniya. Shugaban kungiyar IRA Biram Ould Dah ana tsare da shi tun cikin watan Mayu da ya gabata bayan kona Alkur'ani da wasu mambobin kungiyarsa suka yi. Kotun shari'ar kasar Mauritaniya na zarginsa tare da abokansa 6 kan neman kawo baraka da tashin hankali ga kasa. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku